Daga muhammad muhammad zahraddin
Wata kotu a Turkiyya ta aike da wata fitacciyar ‘yar jarida Sedef Kabas gidan yari saboda zargin ta zagi shugaban kasar.
An kama Kabas a ranar Asabar a Istanbul kuma nan take wata kotu ta ce a kai ta gidan yari kan a fara sauraren kararta.
Ana zarginta ne da gaya wa shugaban kasar Recep Tayyib Erdogan magana ta anyar amfani da karin magana wanda ta fada kai tsaye a wani shiri na gidan talabijin da ke alaka da masu adawa da shugaban. Sai dai ta musanta wannan zargi.
Irin wannan laifin hukuncinsa daurin gidan yari ne na shekara daya ko hudu.