News
Gwamna Buni ya ba da umarnin gudanar da bincike yayin da wani soja ya harbe direban mota a Yobe
daga idirs abubakar
Gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni, ya bayar da umarnin gudanar da bincike kan zargin kashe wani direba Mohammed Toli da sojoji suka yi a Garin Alkali da ke karamar hukumar Bade a jihar.
An harbe Toli ne da yammacin ranar Juma’a a gidan mai a lokacin da ya ke neman tsira.
Buni, a cikin wata sanarwa ta hannun Babban Daraktan Yada Labarai, Mamman Mohammed, ranar Asabar a Damaturu, ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici bayan an dauki tsawon lokaci ana samun zaman lafiya a yankin da kuma jihar.
“Gwamnati da hukumomin tsaro ba za su amince da duk wani aiki na ganagnci da zai iya kawo naƙasu ga zaman lafiya da muka samu ba.
“Saboda haka, ina tabbatar muku da cewa gwamnati za ta binciki lamarin yadda ya kamata, kuma za ta ɗauki matakin da ya dace.
“Ina kuma kira ga al’ummar Ƙaramar Hukumar Bade da ma jihar baki daya da su kwantar da hankalinsu da bin doka da oda.
“Ya kamata mu guji duk wani abu da zai gurɓata mana zaman lafiya. Ina yi muku nasiha da ku kasance Musulmi nagari ku dauki ƙaddara, kamar yadda Allah Ya so kuma ku guji tashin hankali da ƙone-ƙone a kan tituna.
“Allah (SWT) Ya gafarta wa marigayin kurakuransa, ya ba shi Aljannatul Firdaus tare da iyalansa, da juriyar rashin,” in ji gwamnan.
Kanfanin Daillancin Labarai na Ƙasa, NAN ya kuma ruwaito cewa, a safiyar Asabar din nan ne wasu matasa da suka fusata suka rufe yankin Filin Tanda da ke cikin garin Gashua, domin nuna ɓacin ransu biss kisan gillar da aka yi wa Toli.
Sun ƙona tayoyi da wasu kadarori tare da neman a yi wa marigayin adalci wanda suka bayyana a matsayin mai don zaman lafiya da bin doka da oda.
Da aka tuntubi kakakin rundunar ‘yan sandan Jihar Yobe, Dungus Abdulkarim, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce ‘yan sandan sun dawo da doka da oda a yankin.
Abdulkarim, Mataimakin sufritendan ‘yan sanda, ya ce ana kan bincike kan lamarin kuma duk wanda aka samu yana da hannu, to zai fuskanci fushin doka.
