Gwamnatin Jihar Kano ta dakatar da lasisin dukkan makarantu masu zaman kansu har sai an tantance su.
Kwamishinan Ilimi na Kano Sanusi Said Kiru ne ya sanar da hakan a yayin ganawa da manema labarai.
Lamarin na zuwa ne yayin da aka gurfanar da mai makarantar Noble Kids a kotu, wanda ake zargi da kashe Hanifa Abubakar mai shekara biyar a makarantar tasa.
Ya ce za a kafa wani kwamiti na musamman da zai tantance makarantun sannan za ta fitar da matakan da za a yi amfani da su wajen tantance makarantu a jihar.
Kazalika ya ce dukkan makarantun da ba su cika sabbin ka’idojin da za a saka ba, sun tafi kenan – ba za a buɗe su ba.