Connect with us

Uncategorized

2023: Miyetti-Allah ta yi amai ta lashe kan goyon bayan takarar Tinubu

Published

on

Spread the love

Daga Yasir sani Abdullah

 

 

Advertisement

Kungiyar Miyetti Allah Cattle Breeders Association of Nigeria, MACBAN, ba ta zaɓi wani ɗan takarar shugaban kasa a zaben 2023 ba.

Sakataren MACBAN na kasa, Baba Ngelzarma ne ya baiyana haka a wata sanarwa da ya rabawa manema labarai ranar Laraba a Abuja.

Jaridar Daily Nigerian Hausa ta ruwaito cewa, Shugaban kungiyar MACBAN reshen Jigawa, Ya’u Haruna, a ranar Lahadin da ta gabata ya amince da ƙudurin takarar shugaban ƙasa na Tinubu bayan ganawar da suka yi a cibiyar horas da harkokin noma da karkara da ke Abuja.

Advertisement

Sai dai kuma kwatsam sai Ngelzarma ya yi mi’ara-koma-baya, inda ya ce har yanzu ƙungiyar ba ta ware wani mutum da ƙungiyar za ta mara masa baya ba.

Ya ce: “Hankalin shalkwatar MACBAN ta kasa ya kai kan wani labari da ake yadawa a kafafen yada labarai na cewa sun baiyana goyon bayan su ga takarar Bola Ahmed Tinubu.

“Muna so mu baiyana cewa kungiyar ba ta amince da wani dan takara ba.

Advertisement

“Wadanda su ka amince da takarar Tinubu suna yin haka ne a ƙashin kan su ba a ƙungiyance ba. Bai kamata MACBAN ta sanya kanta a cikin siyasar ɗan takara a wannan lokaci ba,” in ji Ngelzarma.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *