News
KDC ta fara wayar da kan malaman Tsangayu a Kano
Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Wata Kungiya mai zaman kanta da ke fafutukar kawo sauyi ga tsarin Ilimi na Almajiri, KDC Foundation, ta dauki nauyin malaman Makarantun Tsangaya, domin tattaunawa da wayar da kan su kan sabon manhajar da ta tsara na tafiyar da makarantun Tsangaya.
Tattaunawar wadda ta gudana a ranar Litinin a Kano, tare da masu ruwa da tsaki daga gwamnatin tarayya da na jiha da malaman makarantu da kafafen yada labarai wanda ya ta ta’allaka ne kan hanyoyin zaburar da malaman Islamiyya, domin su amince da sauye-sauye masu kyau daga manhajar karatu.
Solacebase ta rawaito cewa, shugaban gidauniyar, Khalifa Muhammad Dankadai, ya ce, makasudin taron shi ne domin jin ta bakin malaman Islamiyya kan yadda suke kallon manhajar da kuma samun abubuwan da suka dace, domin tsara yadda ya dace da ra’ayinsu.
Ya ce “Ta hanyar nazarin abubuwan da malaman Islamiyya suka bayar, an tabbatar da cewa sun amince da tsarin kuma a shirye suke su yi aiki da shi a duk lokacin da aka samu wanda shi ne babban damuwarmu. Domin dole ne su yarda kuma su yi aiki tare da tsarin karatun sannan za mu cimma burinmu na gyara tsarin.
“Don haka za mu yi la’akari da ra’ayoyinsu tare da ba su hannu ‘yanci, domin gudanar da tsarin da kansu. Daga cikin abin da za mu yi shi ne koyar da Turanci da Lissafi, da kuma koyar da yara kanana sana’o’in kasuwanci ta yadda za su daina barace-barace a kan tituna da kuma yin ado da kyau kamar sauran daliban,” inji shi.