News
Majalisar wakilai ta amince da zaben ‘yar tinke
Daga Yasir sani Abdullah
Majalisar Dattawa da ta Wakilai a Najeriya sun daidaita matsayar da suka ɗauka game da gyaran Ƙudirin Dokar Zaɓe da Shugaba Buhari ya ƙi saka wa hannu sakamakon sakin layin da ke tilasta jam’iyyu su yi zaɓen ‘yar tinƙe wajen fitar da ‘yan takara.
Idan ba a manta ba, bayan Buhari ya ƙi amincewa da dokar yana mai cewa sai ba su zaɓi, ‘yan majalisar sun ce za su gyara domin samar da zaɓi na zaɓen wakilai da kuma yin sasanci.
Yayin da Majalisar Dattawa ta amince da zaɓukan uku, Majalisar Wakilai ta amince ne da zaɓen ‘yar tinƙe da kuma na wakilai kaɗai. Sai a yau Talata ne majalisar ta samar da hanya ta uku ta zaɓen sannan ta sake amincewa da dokar.
Cikin wani zaman haɗin gwiwa da suka yi ranar Litinin, shugaannin majalisun sun fayyace ma’ana da kuma yadda za a gudanar zaɓen ‘yan takarar ta kowace daga cikin hanyoyi ukun. A cewar
“Mun yi murna da cimma matsaya tsakanin majalisun biyu don haɗuwa kan abu ɗaya kuma muna da ƙwarin gwiwa sosai cewa shugaban ƙasa zai saka mata hannu,” in ji Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmad Lawan.