News
Ranar 17 ga watan Maris za a fara sauraron daukaka karar Inusa Yellow
Daga kabiru basiru fulatan
Kotun daukaka kara da ke garin Fatakwal ta sanya ranar 17 ga watan Maris, domin fara sauraron karar da Yunusa Yellow ya daukaka a gabanta na kalubalantar hukuncin babbar kotun jihar Bayelsa.
Lauyoyin Yunusa Yellow, Sunusi Musa ne ya sanar da hakan a shafinsa na Facebook ranar Talata.
Sauran lauyiyon da za su tsayawa Yunusa Yellow sun hadar da Huwaila Muhammad da Abdul Muhammad Rafindadi, da kuma Kayode Olasebikan.
Idan za a iya tunawa tun a shekarar 2015 ne aka kama Yunusa Yellow bisa zargin sato wata yarinya Ese Oruru da ga jihar Bayelsa zuwa Kano.
Yunusa Yellow dai ya taho da yarinyar Ese ne zuwa Kano suka kuma yi aure, sai dai an kama shi da laifin satar mutane da kuma safarar kananan yara.
Bayan kama shi ne a nan Kano aka kuma aike da shi can jihar Bayelsa garin da yarinyar ta ke domin a yanke masa hukunci.
Babbar kotun jihar dai ta zargeshi da laifuka har guda biyar da suka hadar da garkuwa da mutane da hakkewa karamar yarinya, da kuma yin amfani da dama kan karamar yariwa, sai kuma laifin yin amafani da karancin shekarunta wajen yi mata wayo. Saboda hakan ne kotun ta yanke masa hukuncin daurin shekaru 26 a gidan yari a can Bayelsa.
Sai dai da yake yanke hukunci alkalin kotun, Jane Inyanga, ta ce, Yunusa bai aikata laifi na farko ba wato garkuwa da mutane.