News
Yadda ‘yan sanda suka kama mutum huɗu bisa zargin dukan wata mata a Maiduguri
Daga muhammad muhammad zahraddin
Rundunar ƴan sandan Najeriya ta ce ta kama mutum huɗu cikin tara waɗanda ake zargi da kai hari shagon abincin wata matashiya da ke babban wajen wasan yara na Jihar Borno.
A cikin makon nan ne dai wani bidiyo ya rinƙa yawo a shafukan sada zumunta wanda ya nuna yadda wasu mutane suna zabga wa wata mari da kuma zaginta.
Wadda aka rinƙa duka a bidiyon mai suna Fadila Abdulrahman, na da shagon sayar da abinci ne mai suna Zuhura Restaurant a Maiduguri, inda waɗanda suka ci mutuncin nata suka rinƙa iƙirarin cewa ta yi wa ɗan majalisa Ahmed Satomi butulci.
Sai dai Ahmed Satomi ya musanta batun, tare da cewa ba shi da wata alaƙa da wadanda suka aikata wannan lamari.
Bayan dukan da ta sha, wasu hotuna da Fadila ta wallafa a shafin Facebook sun nuna yadda matasan suka yi kaca-kaca da wajen sayar da abincin nata.
Mutane da dama a shafukan sada zumunta sun nuna ɓacin ransu kan wannan lamari da kuma kira da a bi mata haƙƙinta.
A wani saƙo da ta wallafa a shafinta na Facebook, ta bayyana cewa wasu mutane ne da ba ta san ko su wane ne ba suka je shagonta a cikin Keke Napep inda suka tambaye ta ko tana biyan gwamnati haraji a inda ta kafa shagonta, amma a cewarta, tuni ta daddale da babban manajan wajen wasan yaran na Jihar Borno kan lamarin.
Ta bayyana cewa mutanen sun shaida mata cewa hukumar kula da filaye da safayo ta jihar ne suka turo su domin rushe shagonta cikin minti 30, amma a cewarta, tana ganinsu ta san ƴan daba ne.
A cewarta, nan take mutanen suka fara fasa shagon nata inda ta ce a lokacin da suka soma, sai ta fara faɗa da su inda su kuma suka rinƙa dukanta da zaginta har suka rushe shagonta.
INDARANKA ta tuntuɓi Fadila Abdulrahman domin jin ƙarin bayani amma ba mu same ta ba.