Gwamnatin tarayya ta bayyana bukatar neman karin naira tiriliyan 2.557 don samar da kudaden tallafin mai dori akan naira biliyan 443 da aka amince da shi a kasafin kudin 2022.
Sai dai cikin wata sanarwa da PDP ta fitar dauke da sa hannun Sakataren yada labaranta na kasa, Debo Ologunagba, ta zargi APC da shirin karkata akalar kudaden don yin amfani da su a zaben da ke tafe.
A cewar Ologunagba, gwamnatin ta APC ta saba irin wannan cushe don biyan bukatunta.
“PDP na da labarin yadda shugabannin APC ke cusa batun neman karin naira tiriliyan 2.557 akan naira biliyan 443 da aka riga aka amince da shi a kasafin kudin 2022 don su samar da rarar makudan kudade ga shugabannin APC, wadanda za su raba su kuma yi amfani da su wajen yin magudi a zabukan 2023.” Ologunagba ya ce.
Ya kara da cewa, duk da cewa PDP na goyon bayan tallafin mai, amma jami’yyar ba ta yarda da wannan karin kudade ba yana mai kira da majalisar dokoki ta yi watsi da wannan bukata.
Sai dai cikin wata hira da ya yi da Muryar Amurka, Kakakin shugaba Buhari, Malam Garba Shehu, ya ce kamfanin NNPC ya ba da kiddidgar wadannan kudaden da ake bukata.
“Magana daya ce, kamfanin mai na kasa (NNPC) ya kididdge cewa, ana bukatar naira tiriliyan uku don cimma gibi akan man da ake shigowa da shi Najeriya ana sayar da shi akan farashi mai sauki.”
A cewar Malam Shehu, dole sai gwamnati da majalisar dokoki sun hada kai don ganin yadda za a samu wadannan kudade idan har ana so a ci gaba da sayar da mai a farashi mai rahusa ga ‘yan kasa.