Hukumar kwastam a Najeriya ta kama hodar ibilis kilo 11.913 wadda aka ƙiyasta kuɗinta da kusan naira biliyan uku da miliyan ɗari tara.
Mai magana da yawun hukumar reshen Seme da ke kan iyaka da Jamhuriyyar Benin ne ya sanar da kamen.
DSC Hussaini Abdullahi ya kuma bayyana cewa sun kama jarkokin man fetur dubu ɗaya da ɗari shida da sittin da biyar wanda kuɗinsu ya haura miliyan goma.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar ta ƙaddamar bincike na musamman domin daƙile sumoga da ake yi na man fetur kan hanyoyin Seme da Badagry.