News
Ƙusa a APC a Gombe, Jamilu Gwamna ya fice da ga jami’yar
Daga kabiru basiru fulatan
Tsohon mai neman takarar Gwamna kuma ƙusa a Jam’iya mai mulki ta APC a Jihar Gombe, Jamilu Isyaku Gwamna ya yi murabus da ga jami’yar.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa Gwamna, wanda ya ke da ƙudurin tsayawa takarar gwamnan jihar a zaben 2023, ya mika wasiƙar murabus din sa da ga jami’yar ga Shugaban APC na mazaɓar Jekadafari a jiya Talata.
A wasikar, wacce wakilin Daily Nigerian Hausa ya gani a yau Laraba, Gwamna ya shaida cewa sai da ya tuntuɓi iyalansa, abokan siyasarsa da magoya baya sannan ya ɗauki matakin.
Duk da bai fadi dalilan da su ka sanya ya fice daga jam’iyar ba, majiyoyi da ke da kusanci da Gwamna sun shaidawa wakilin mu cewa shugabannin jam’iyar a jihar goyon bayan gamwan mai ci, Inuwa Yahaya su ke yi a jihar.
Isah Kaltungo, ɗaya daga cikin alna jikin Gwamna ya shaida cewa a wasu daga Ƙanan Hukumomin da gwamna Yahaya ya kai musu ziyara, jagororin jam’iyar sun nuna shi su ke so ya zarce zuwa zangon mulki na biyu.
A cewar sa, wannan wata manuniya ce cewa jam’iyar ba za ta yi adalci ga masu neman kujerar gwamnan ba a zaɓen fidda gwani da za a yi nan gaba.
Sai dai kuma har yanzu gwamna bai shiga wata jam’iyar ba.