Connect with us

News

Muhiyi Magaji ya maka Ganduje a kotu

Published

on

Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Advertisement

Dakataccen Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimingado, ya maka Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje a kotun masana’antu sakamakon dakatar da shi da a ya yi matsayin shugaban hukumar.

Rimingado ya shigar da ƙarar gwamnan, da kuma sauran mutane biyar a kotun a yau Laraba.

Sauran biyar ɗin da ya shigar da ƙarar sun haɗa da Majalisar Dokoki ta Jihar Kano, Akanta-Janar na Jiha, Shugaban Hukumar Yaƙi da Cin-hanci da Rashawa na Riƙon Ƙwarya, Kwamishinan Ƴan Sanda na Kano, a matsayin wanda a ke ƙara na 1, 2, 3, 4, 5, da na 6.

Advertisement

Rimingado ya shigar da ƙarar ne a gaban kotun, ƙarƙashin jagorancin Alƙali, Oyejoju Oyewumi.

Lauyan mai ƙara, Muhammad Tola, ya shaidawa kotun cewa dukkan mutum shidan da a ke ƙara an kai musu takardar ƙarar amma kuma har yanzu basu zo kotun ba.

Ya kuma shaidawa kotun cewa akwai wasu bukatu da ya ke so ya janye su a kotun.

Advertisement

Da ya ke martani a bisa rokon lauya mai karan, lauyan waɗanda a ke ƙara na 1,2 da na 4, Abdulsalam Saleh ya ce sun aika da buƙatar cewa waɗanda su ke karewa ba lallai sai sun je kotun ba.

Saleh ya kuma ƙara da cewa su na shirin ɗauke ƙarar zuwa ga reshen kotun a Kano sabo da a Kano abin ya faru kuma waɗanda a ke ƙara su ka a Kano su ke.

A nata jawabin, Tola ta tambayi Saleh dalilin da ya sa ba a shigar da ƙarar a Kano ba.

Advertisement

Ta ƙara da cewa duk da ta ja hankalin shugaban Kotun a kana haka, amma an bata umarnin ta jagoranci ƙarar.

Ta ƙara da cewa an shigar da ƙarar ne a Abuja saboda gudun rikici tsakanin magoya bayan mai ƙarar da kuma na Gwamnati.

Alkakiyar ta dage zuwa 7 ga watan Maris domin sake zaman kotun.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *