Connect with us

News

Shari’ar Abduljabbar ta sanya Muaz Magaji zai ƙara kwana ɗaya a gidan yari

Published

on

FB IMG 16438303489732720
Spread the love

Daga Muhammad Muhammad zahraddini

 

 

Advertisement

Tsohon Kwamishinan Aiyuka da Gine-gine na Jihar Kano, Muaz Magaji zai ƙara kwana ɗaya a gidan yari, inda a ka ɗaga sauraron ƙarar tasa da ga Alhamis 3 ga watan Febrairu zuwa Juma’a 4 ga wata.

Shi dai Magaji, wanda a ka fi sani da Ɗan Sarauniya, na shan tuhumar Laifuka huɗu da su ka haɗa da ɓata suna, cin zarafi, cin mutunci da kuma tada hankali ga gwamnan Kano Abdullahi Ganduje.

Sai dai kuma ya nisanta duka laifukan da a ke tuhumar sa da su, waɗanda su ka saba da sashi na 392, 399 114 na kundin dokar kaifuka ta 1999 ta Kano.

Advertisement

Bayan an zauna sauraron ƙarar, sai alƙalin kotun majistire mai lamba 58, Aminu Gabari ya bada umarnin aike da Magaji, babban ɗan adawar Ganduje, gidan yari har sai 3 ga Febrairu domin sauraron bukatar da a ka shigar ta bada belin sa.

Sai dai kuma a wata wasika da a ka aikewa lauya Magaji, wacce rijistaran kotun da ke Nomansland, Aminu Tudunwuzirci ya sanyawa hannu, kotun ta dage zaman nata saboda tsaro.

Kotun ta ce ƙarar Magaji ta haɗe da ta Abduljabbar Nasiru Kabara a gobe Alhamis.

Advertisement

Kotun ta ƙara da cewa saboda da dalilin tsaro kuma jami’an tsaron da za a kai a kotun Nomansland ɗin su je dai za a kai babbar kotun shari’ar Muslunci ta Kofar Kudu inda a ke shari’ar Abduljabbar.

“Sabo da haka an dage zaman wannan shari’ar sai ranar juma’a, 4 ga watan Febrairu da karfe 2:30 na rana,” in ji wasiƙar.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *