Connect with us

News

Alfanun bututun iskar gas na A-K-K ga Arewacin Najeriya

Published

on

Spread the love

 

Daga: yasir sani abdullahi

 

Advertisement

 

A shekara ta 2020 ne Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ya buɗe aikin bututun iskar gas na Ajaokuta-Kaduna-Kano (wanda aka fi sani da AKK). Bututun zai taso ne daga Ajaokuta(da ke jihar Kogi) ya bi ta Abuja da Kaduna sannan ya isa Kano. Ana sa ran cewa nan gaba bututun ya kai har Algeriya.

Shi dai wannan bututu mai nisan kilomita 614 zai laƙume kuɗi har dalar Amurka biliyan biyu da miliyan 800 (2.8 billion USD). Wannan ya nuna cewa wannan aiki na AKK shi ne mafi girma da gwamnatin tarayya take yi a faɗin Najeriya.

Advertisement

Na lura cewa mutane da yawa ‘yan Arewa ba su san wannan aiki da kuma alfanun da ake sa ran zai kawo mana ba. Mun daɗe muna ƙorafi a kan rashin wutar lantarki wanda hakan ya durƙusar da kamfanoni masu yawa, ya kuma hana samar da wasu sababbi. Rashin irin wannan bututu shi ne ya sanya mu cikin wannan ƙangi. Manya-manyan kamfanoni irin su Ɗangote Cement and Indorama Fertilizer ba da wutar NEPA suke samar da lantarkinsu ba. Suna da ƙananun cibiyoyi na samar da wutar a cikin kamfanonin nasu. Waɗannan cibiyoyi suna amfani da iskar gas, wanda hakan ya fi araha idan aka gwada shi da man dizel. Hakn ne ya sa irin waɗannan kamfanoni suke ta ƙara yawaita a kudancin Najeriya. Yanzu haka, Najeriya tana da bututun iskar gas kusan kilomita 2000 wanda kusan kashi 90/100 yana kudu ne. Ɗaruruwan masana’antu ne suke amfana da wannan bututu a kullu-yaumin

Idan aka samu kammala wannan babban aiki na AKK, zai ba da dama irin waɗannan manyan kamfanoni da yawa za su shigo Arewa wanda hakan zai taimaka wajen bunƙasa tattalin arziki, iai kuma rage rashin aikin yi ta hanyar sama wa dubunnan matasa aikin yi.

Wataƙila a ‘yan kwanakin nan za ku lura da wasu tireloli a manyan tituna da rubutu “Greenville” a bodinsu. Waɗannan tireloli suna ɗauke ne da iskar gas wanda aka sarrafa shi ya koma kamar ruwa (a Turance, liquefied natural gas). Saboda rashin bututun gas, dole sai dai a yi dakon sa a kai su kamfanoni a inda za a sake mayar da shi iskar gas don samar da wutar lantarki. Kamfanonin da suke amfani da irin wannan ruwan gas sun haɗa da Mamuda Industries (masu Pop Cola) da Aspira (masu omon Viva) dukkansu a Kano. Shi ma BUA Cement da ke Sokoto yana gina irin wannan cibiyar mai ƙarfin megawatt 86.

Advertisement

A yanzu haka dai ana ta aikin wannan bututu. Duk wanda yake wucewa ta Marabar Jos da ke kusa da Kaduna zai ga zangon ‘yan kwangilar, inda kullum ake ta hada-hadar aikin. Sai dai wani hanzari-ba-gudu-ba, kamar yadda na ga Salihu Tanko Yakasai ya yi bayani a kwanakin baya, an samu tsaiko wurin samun bashi daga ƙasar Sin, kasantuwar su ne za su bayar da 85% na kuɗin. Fatanmu, gwamnatin tarayya ta ƙara ƙaimi wurin ganin an samo waɗannan kuɗaɗe don aiwatar da wannan muhimmin aiki.

Su ma gwamnoni, da sarakuna da masu faɗa-a-ji suna da muhimmiyar rawar da za su taka. Muna kiran su da su yi amfani da kujerun da Allah Ya ba su wajen matsa lamba ga duk wasu masu ruwa-da-tsaki a wannan aiki. Idan Allah Ya taimake mu, sai a iya cin ƙarfin aikin kafin wa’adin wannan gwamnati ya ƙare.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *