Connect with us

News

Gwamnatin Kano ta bankaɗo inda a ke yin jabun man girki

Published

on

FB IMG 16438850172283454
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Advertisement

Hukumar Kare Haƙƙin mai Sayen Kaya ta Jihar Kano, KCPC, ta bankaɗo wani waje da a ke haɗa jabun man girki a jihar.

Manajan-Daraktan hukumar, Janar Idris Bello Danbazau mai ritaya, shine ya baiyana haka a wata sanarwa da kakakin hukumar, Musbahu Yakasai ya sanyawa hannu a jiya Laraba.

Sanarwar ta ce, Danbazau, wanda ya samu wakilcin mataimaki na musamman ga gwamnan Kano kan 6wbbatwr da ingancin aiyuka da kayayyaki, Sale Muhammad ne ya ja tawoga da ga Hukumar su ka kai ziyarar gani da ido a wajen da a ke haɗa jabun man da ke Dakata Rinji a Ƙaramar Hukumar Nassarawa a jihar.

Advertisement

A cewarsa, wajen da a ke haɗa man ma a kusa da wata makekiyar bola ya ke, inda ya ƙara da cewa wajen ba shi da tsafta da kariya ga kamuwa da cutuka ga al’umma.

Ya ce hukumar ba ta da niyyar ta durkusar da kasuwancin al’umma sai dai kawai ta na ƙoƙarin kawo gyara da tsafta ne domin amfanin al’umma.

A sanarwar, Danbazau ya ƙara da cewa bankaɗo wajen haɗa jabun man girkin 2ani yunƙuri ne na gwamnatin Kano na ta kare al’umma da ga cin gurbatattaun kayaiyaki domin lafiyar su.

Advertisement

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a bara ne dai a ka samu rasuwar mutane da dama a wasu ƙananan hukumomi na jihar bayan da su ka sha wani gurbataccen sinadarin haɗa lemo, wanda a ke kira da ɗan tsami.

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *