Entertainment
Da Zarar Nayi Aure Zan Dena Harkar Fim -Jaruma Maijidda Abbas
Daga kabiru basiru fulatan
Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina finai ta Kanywood, Maijidda Abbas ta bayyana cewa da zarar ta yi aure za ta dena harkar fim.
Jarumar wacce ita ce jami’ar walwala ta kungiyar MOPAN ta bayyana hakan ne yayin tattaunawa da jaridar Prime Time News Hausa a Kano.
Tun da farko jarunar ta bayyana cewa ta shigo harkar finai finan Hausa shekaru 18 da suka wuce.
“Shekara kusan 18 kenan na shigo harkar Fim. Abinda ya kawoni Kano karatu nazo yi, da nazo kuma sai na fara mu’ammala da ‘yan fim daga nan kuma sai na shiga harkar.”
Jarumar ta ce mu’ammala da kawance ne yaja hankalinta har ta shiga harkar Fim, sannan ta ce tayi aure a baya daga bisani kuma ta dawo harkar fim din.
Dangane da batun Aure kuwa, Maijidda Abbas ta ce ta kusa yin aure kuma da zarar ta yi aure zata ajiye harkar Fim dama shugabanci a kungiyar ta MOPAN.
“Bana tunanin zan kai babbar Sallah ban yi aure ba, da nayi aure zan hakura da harkar Fim, inji ta.
Haka kuma, ta shawarci jarumai mata masu tasowa da su dinga yi biyayya ga manyansu domin biyayya ce matakin nasara.