Entertainment
Mutane na ta sanyawa Ali Nuhu albarka kan yadda ya yiwa wata mai tallar awara goma ta arziki lokacin da ta yi bari
Daga mujahid dallami garba
Mutane na ta sanyawa jarumi Ali Nuhu albarka, kan yadda ya tallafawa wata yarinya mai tallar awara goma ta arziki, bayan ta yi barin awara…
Duk da irin suka da kahon zuka da akan kafa akan jaruman masana’antar Kannywood wani lokacin sukan yi abin da wasu daga cikin al’umma ke yaba musu gami jinjina musu da fatan su zama abin koyi ta wannan fanni.
Wadanda suka fi samun wannan yabo sun hada da Hadiza Gabon, Mansurah Isah, Ali Nuhu, Adam A Zango, Aisha Humaira da dai sauran su.
A wannan karon jarumi Ali Nuhu ne yayi wani abin arziki, inda abokin sana’arsa, Abdul Saheer, wanda aka fi sani da Malam Ali a cikin shirin “Kwna Casa’in” ya wallafa a shafinsa cewa wani abokinsa ya bashi labarin abin kirkin da yayi akan idon sa, inda ya rubuta cewa:
Ali Nuhu ya yi sharhi a kasan rubutun
Bayan wallafa wannan rubutu, mutane da dama sunyi ta tofa albarkacin bakin su, inda hadda shi jarumi Ali Nuhu ya ce wani abu, inda yayi sharhi da cewa.
“Na gode, Allah ya sa mu dace gaba daya.