Sports
Kasuwar ƴan ƙwallo: Arsenal za ta yi cefanen £ milyan 180, makomar Ronaldo, Osimhen da Zidane
Daga
muhammad muhammad zahraddin
Tottenham za ta yi yunkurin dauko dan wasan Napoli Victor Osimhen a bazara bayan da kulob din na Italiya ya yi watsi da tayin dan wasan Najeriyar mai shekara 23 a watan Janairu. (Fooball Insider)
Arsenal na shirin kashe kusan fam miliyan 180 a wannan bazarar don siyan dan wasan Wolves na Portugal Ruben Neves da dan wasan Everton na Ingila Dominic Calvert-Lewin, dukkansu ‘yan shkara 24, da kuma dan wasan gaban Real Sociedad na Sweden Alexander Isak, mai shekara 22. (Sun).
Newcastle za ta farfado da sha’awarta ta neman dan wasan Lille Sven Botman, mai shekara 22, idan kulob din ya kaucewa ficewa daga gasar Premier bayan da ta kasa samun dan wasan bayan Holland a watan Janairu. (Athlentic}
Sai dai Botman yana jan hankalin Tottenham, wadanda kuma suke sa ido kan dan wasan bayan Inter Milan da Italiya Alessandro Bastoni, mai shekara 22, da Josko Gvardiol na Croatia, mai shekara 20, wanda ke a RB Leipzig. (Telegraph)
Dan wasan gaban Portugal Cristiano Ronaldo, mai shekara 36, zai jira har sai Manchester United ta bayyana sunan sabon kocinta kafin ya yanke shawarar ko zai ci gaba da zama a Old Trafford. (ESPN)
Leeds na da kwarin gwiwar kulla yarjejeniya da dan wasan Brazil Raphinha kan sabon kwantiragi da zai sanya dan wasan mai shekaru 25 ya zama dan wasa mafi karbar albashi a Elland Road. (Football Insider)
Kofar Roma a bude take don sauraron tayin dan was anta na Italiya icolo Zaniolo, kuma Juventus da Tottenham a cikin kungiyoyin da ke zawarcin dan wasan mai shekaru 22. (Calciomercato)
Kociyan kungiyar Thomas Frank ya ce Christian Eriksen da ya koma Brentford kyauta zai iya zama dan wasa mafi girma da kungiyar ta taba kulla yarjejeniya da shi.
Dan wasan tsakiya na Faransa Tanguy Ndombele ya ce rayuwarsa ta Tottenham ba ta kare ba bayan dan wasan mai shekaru 25 ya koma Lyon a matsayin aro. (RMC Sport)
West Ham za ta nemi dan wasan Arsenal dan kasar Faransa William Saliba, mai shekara 20, wanda ke zaman aro da Marseille, a bazara. Ana kuma danganta Saliba da Inter Milan da AC Milan da kuma Real Madrid. (Jeunes Footeux)
Liverpool za ta iya sake neman Fabio Carvalho a bazara bayan kiris ya rage ta sayi dan wasan na Fulham a watan da ya gabata. Sai dai kungiyoyin kasashen waje za su biya diyya kadan kan matashin dan kasar Ingila, mai shekara 19, wanda hakan ya sa Real Madrid, da Barcelona,da Sevilla, da Borussia Dortmund da AC Milan suka dan jinkirta. (AS- in Spanish)
Tsohon kocin Real Madrid Zinedine Zidane, mai shekara 49, har yanzu bai amince ya zama magajin Mauricio Pochettino a matsayin kocin Paris St-Germain ba, yayin da yake jiran ko Didier Deschamps zai bar aikinsa na kocin Faransa. (RMC In Frnchi)