News
Dalilin da ya sa ba mu rantsar da shugabannin jami’ya na Kano ba — APC
Daga kabiru basiru fulatan
Uwar Jam’iyar APC ta Ƙasa ta faɗi dalilin da ya sanya ba ta rantsar da shugabannin jam’iyar na Jihar Kano ba.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa a ranar Alhamis da ta gabata ne dai jam’iyar ta rantsar da shugabannin jam’iya na jiha a jihohi 34 amma banda Kano da Sokoto.
Da ya ke bayani a kan dalilan da ya sanya ba a rantsar da shugabannin jam’iya na Kano ba a jiya Juma’a a Abuja, Sakataren Kwamitin Riƙo na APC na Ƙasa, John Akpanudoedehe, ya ce babu wani abin damuwa a kan matakin.
A cewar sa, uwar jam’iyar ta ɗauki matakin dakatar da rantsar da shugabannin jam’iya na Kano ne domin amfanin ƴan jam’iyar, jihar da kuma ƙasa baki ɗaya.
Ya ce APC na son zaman lafiya kuma Kano ta zama kamar nan ne Shalkwatar jam’iyar, inda ya ce ba za a yi wani abu da zai kawo naƙasu ga zaman lafiyar jam’iyar a jihar ba.
Akpanudoedehe ya ƙara da cewa akwai maganar shari’ar jam’iyar a kotu, sabo da haka uwar jam’iyar ba a ta yi wani abu na kuskure ba.
Sai dai kuma Akpanudoedehe bai fadi dalilin da ya sa jam’iyar ba ta rantsar da shugabannin jam’iya na Sokoto ba.