An sanar da Shugaban ƙasar Senegal Macky Sall a matsayin sabon Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afrika.
Shugaba Sall ya karɓi jagorancin ƙungiyar daga hannun Shugaban Jamhuriyyar Dimokraɗiyyar Kongo, Antoine Felix Tshisekedi.
Mista Tshisekedi ya miƙa jagorancin ne a yau Asabar a yayin taron ƙungiyar na 35 da ake yi a Addis Ababa.
Shugaban hukumar gudanarwa ta Ƙungiyar Tarayyar Afrika, Moussa Faki Mahamat ya yi wa sabon shugaban murna inda ya ce yana fatan ƙwarewar da yake da ita za ta sa ya yi aiki tuƙuru ga nahiyar duk da cewa nahiyar na fuskantar matsain tattalin arziki da kuma ƙalubale a fannin lafiya.