Shugaban ya wallafa hakan ne cikin wani sakon Twitter inda ya ce an gwada shi an kuma tabbatar ya kamu da wannan cuta.
Ya kuma kara da cewa matarsa Emine Erdoğan itama an gwada ta tana dauke da cutar.
Shugaba Erdoğan ya ce zai ci gaba da gudanar da ayyukansa daga gida a matsayinsa na shugaba.
Shugaba Erdogan ya kai wata ziyara ta musamman ne Ukraine tare da matarsa a karshen wannan mako.