Connect with us

News

Hisbah Sun Kai Samame a Gidajen Da a ke Zargin Ana Karuwanci a Fansheka

Published

on

FB IMG 16441248411681990
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Advertisement

Dakarun hukumar Hisbah sun kai sumame a rukunin wadansu gidaje, bisa zargin ana amfani da gidajen wajen aiwatar da karuwanci da sayar da giya, a unguwar panshekara.

A ya yin sumamen Dakarun sun yi nasaran Kamo samari da yan mata a rukunin gidaje guda 10 a lokacin da su ke tsaka da tafka badala.

A nasihar sa ga wadan da aka cefke, Babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya ce, Dakarun sun kai sumamen ne, a sakamakon korafin da jama’a mazauna wadan nan rukunin gidajen unguwar panshekara su kai hukumar Hisbah, kuma binciken, jami’an ya tabbatar da korafin da jama’ar.

Advertisement

Babban kwamandan hukumar Hisbah yayi alkawarin daukan dukkan matakan da ya kamata domin, dakile yaduwar barna a jihar Kano.

Ya na bayanin cewar doka a jihar Kano ta haramata sanar’ar yin karuwanci da sayar da giya ko sha da yin tusarrafi da giya duka doka ta hana kuma laifi ne aiwatar da hakan.

A wani cigaban Dakarun hukumar Hisbah sun sake kai wani sumamen tare da yin nasara kamo motcin guda hudu makare da nau’i daban daban na kwalaben barasa a lokuta da ban da ban da masu yin kurin shigowa da giyar cikin birnin Kano ke yi, a tsakanin titinan kan iyar shigowa Kano da sauran makwabtan jihohi watau kwanan dangora da titin kiru zuwa madobi da kuma titin Zaria zuwa Kano.

Advertisement

A lokacin sumamen an Kamo motoci, guda hudu, makare da kwalaben giya, daga ciki da akwai mota mai kirar Toyota heniec guda biyu, daya na dauke da kwalabe dubu biyu da Dari hudu (2400) na kwaleben nau’ikan barasa dayar kuwa ta dauko katan kantan na giyar gwangwani da wata karamar mota kiran Toyota kuma ta na dauke kwalabe dubu daya da Dari takwas (1800) na giyan da babbar mota rufaffiya.

Babban kwamandan hukumar Hisbah, Dr. Harun Muhammad Sani Ibn Sina ya kara yin jinjina ga Dakarun sa bisa narar, da su ke samu kuma ya bai yana nasarar da hukumar ke samu a kai a kai, bisa hadin kai da goyon bayan da jama’a ke bawa Dakarun da sauran jami’i a lokacin da su ke kukarin gudanar da aiyukan su a fadin jihar Kano.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *