Gobara ta tashi a cocin Africa Ta Kudu ta Saint George’s Cathedral, inda a nan ne aka binne gwarzon yaƙi da wariyar launin fata Archbishop Desmond Tutu.
Wutar ta soma ne a ginin ƙasa na cocin da ke a Cape Town – kuma ana kyautata zaton da gan-gan aka tayar da gobarar.
Mahukunta sun ce an samu nasarar kashe wutar duk da cewa ta ɗan yi ɓarna.
Shugaban cocin Michael Weeder ya ce an hango wani yana guduwa bayan ya jefa wani ƙyale da ke cin wuta ta taga.
Tuni aka kama mutumin amma ya musanta zargin da ake yi masa.