Wata tankar mai ta kama da wuta a Ƙaramar Hukumar Soba da ke Jihar Kaduna.
Waɗanda suka shaida lamarin sun bayyana wa BBC cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe goma na safiyar Lahadi a lokacin da tankar ta kai mai a gidan man Shirash da ke hanyar Jos.
Babu tabbaci kan yadda wutar ta tashi sai dai shaidu sun ce tana cikin sauke man fetur ta kama da wuta, haka kuma babu wanda ya jikkata ko kuma ya rasa ransa.
Rahotanni sun ce motocin kashe gobara har uku sun kai ɗauki inda suka taimaka wurin kashe wutar.
Haka ma jami’an tsaro sun je wajen da lamarin ya faru domin sa ido.
Ko a watan Janairun da ya gabata, sai da aka yi gobara sau 114 a yankunan Kaduna da Zaria da kuma Kafanchan duk a Jihar Kaduna kamar yadda hukumar kashe gobara ta jihar ta bayyana.