News
Mata Musulmi sun yi gangamin wayar da kai a kan hijabi a Abuja

Daga yasir sani abdullahi
Musulmai mata da ga ƙungiyoyi daban-daban, ƙarƙashin inuwar Gamaiyar Matan Musulmi na Nijeriya, a yau Asabar sun yi wani gangami a Unity Park a Abuja domin wayar da kan al’umma kan amfanin hijabi.
Sun yi kira ga hukumomin gwamnati da su tashi tsaye wajen kare mata masu sa hijabi da ga kyarata, ƙyama da kuma nuna bambanci.
Ɗaya da ga cikin matan, Azeeza Jibrin ta baiyana cewa hijabi ya kasance sutura ce ta mutunci da tarbiyya, inda ta jaddada cewa sanya hijabi ga mace ibada ne.
Jibrin ta yi kira da a ƙyale mata Musulmi su riƙa yin abinda addinin Musulunci ya hore su da su yi in dai abin da su ke yi bai saɓawa Shari’a ba.
Ta kuma yi kira ga Gwamnati da ta samar da yanayi mai kyau da mata za su riƙa aiwatar da ibadar su ta Musulunci cikin kwanciyar hankali ba tare da kyarata b, in da ta yi kira da a amince da ƙudurin Dokar Hana nuna Bambancin Addini 2021.
Ta kuma yi kira ga mata Musulmi da kada su ci gaba da sanya hijabi, kada su karaya da kyarata da nuna ƙyama da bambanci.