News
Kwamishina a Sokoto ya tallafawa mata 50 da naira dubu 200 kowaccen su
Daga Muhammad Muhammad zahradd
Kwamishinan Kuɗi na Jihar Sokoto, Abdussamad Dasuki ya rabawa mata 50 Naira dubu 200 kowaccen su a matsayin jari domin yin sana’o’i, a ƙarƙashin shirin sa na tallafi da koya sana’a mai taken #WorkYourWayYourself.
Waɗanda su ka amfana sun fito ne da ga mazaɓu 11 da ga ƙaramar hukumar Tambuwal ta jihar.
Da ya ke raba tallafin, Kwamishinan, wanda ya samu wakilcin Shugaban Ƙaramar Hukumar Tambuwal, Nasir Babata, ya hori matan da su yi amfani da kuɗin ta hanyar da ta dace.
A cewar sa, duk da cewa gwamnati za ta ci gaba da tallafawa mata a jihar, lokaci ya yi da za su tsaya da ƙafar su.
Kwamishinan ya ce wannan tallafin somin-taɓi je kamar yadda tsarin gwamnatin Gwamna Aminu Waziri Tambuwal ya tanadar.
“Sabo da haka kowa zai sharɓi romon domokraɗiyya kuma ku ci gaba da amfani da tallafi da a ke baku yadda ya dace,” in ji shi.