Connect with us

News

Miji ya harbe matarsa lokacin da a ke musu sulhu

Published

on

FB IMG 16442989061636941
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Advertisement

Wani fustattacen miji, Shams Sharif ya harbe mai ɗakinsa da wasu mutum uku a dangin ta sannan shima ya harbe kansa yayin da a ke musu sulhu a Cairo, makonni kaɗan bayan auren su.

Aljazeera Arabic ta rawaito cewa a ranar Juma’a, Sharif, ɗan shekara 22 kacal da haihuwa, ya ɓoye bindiga a cikin jaka yayin da zai halarci zaman sulhun tsakanin danginsa da na matar.

A lokacin da tattaunawar ta yi zafi yayin da a ke ƙoƙarin sulhun, sai Sharif sai ya fusata ya kuma zato wannan bindiga ya ɗorawa matar ta sa, Nour Ghazal, yar shekara 20 da mahaifiyarta, Nona Mohamed, mai shekara 58.

Advertisement

Kafafen yaɗa labarai na cikin gida sun baiyana cewa Sharif ya kuma bindige ƙanwarsa, Sherine, mai shekara 42 da mijinta, Khaled Mohamed mai shekara 53 da ga bisani shima ya hallaka kan sa.

Bayan da maƙota su ka ji ƙarar harbin, sai su ka yi maza su ka shaidawa ƴan sanda, amma ko da su ka zo gidan, sai su ka tarar dukkan su sun mutu.

Mijin, wanda ya ke harkar lalatattun kayaiyaki, an ce ya an taɓa kwantar da shi a asibitin ƙwaƙwalwa a watannin da su ka gabata kafin ya aikata kisan.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *