News
Kwankwaso, Naja’atu Mohammed da Kingsley Moghalu Na Shirin Kafa Sabuwar Jam’iyyar Maja a Wannan Watan
Daga yasir sani abdullahi
Wasu shugabannin siyasa da masu ruwa da tsaki na shirin kafa wata sabuwar jam’iyya da zata zama jam’iyya mai karfi bayan APC da PDP a mako mai kamawa.
Wadanda ke shirin kafa jam’iyyar sun hada da: Farfesa Pat Utomi, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Farfesa Kingsley Moghalu, Sanata Saidu Dansadau da Hajiya Naja’atu Mohamamed da Farfesa Remi Sonaiya da Fasto Ituah Ighadalo da Farfesa Osita da sauransu.
Shugabannin sun amince da hakan ne yayin taron da ya gudana kan kafa sabuwar jam’iyya da zata zama karin zabi a siyasa da ya gudana a birinin Lagos ranar Lahadi.