News
Rikicin APC a Kano: Ba za mu yarda da rashin adalci a rabon muƙaman da uwar jam’iya za ta yi ba — Shekarau
Daga yasir sani abdullahi
Ɓangaren Jam’iyar APC a Jihar Kano, wanda Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta ya ce ba zai yarda da rabon muƙaman da uwar jam’iya ta ƙasa za ta yi tsakanin su da tsayin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ba sai dai idan za a yi gaskiya da adalci.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa, a ci gaba da zaman sulhu tsakanin ɓangarorin biyu da su ke ta gabza rikicin mallakar jam’iyyar tun bayan kammala zaɓen shugabannin jam’iya, a ranar Asabar ne dai Kwamitin Riƙo na APC ya kira jagororin biyu da su je Abuja domin wata ganawa ta gaggawa.
Bayan tashi da ga taron gaggawar, ƙarƙashin jagorancin Mai Mala Buni, Gwamnan Jihar Yobe, jam’iyyar ta yanke shawarar tura wani kwamiti mai ƙarfi zuwa Kano domin tabbatar da an bi sabon tsarin rabon muƙaman jam’iyyar daidai.
A wata taƙaitacciyar sanarwa bayan taron na jiya Asabar da daddare, mai magana da yawun Shekarau, Sule Ya’u Sule, ya tabbatar da cewa jam’iyyar ta samar da tsarin sanya kowa cikin harkokin jam’iyyar ta APC a Kano.
A cewar Sule, a yau Litinin za a sanar da duk ɓangarori biyun halin da ake ciki.
Sannan a jiya Lahadi, Sahekarau ya yi kira ga magoya bayan jam’iyar da su kwantar da hankali su kuma baiwa uwar jam’iyar goyon baya, inda ya ƙara da cewa za su bi umarnin Ubangiji da kuma na jam’iya su yarda a yi sulhu da tsafin Ganduje.
Sai dai kuma a jiya Lahadin da daddare, a wata sanarwa da ƴan tsafin Shekarau ɗin su ka sanyawa hannu, sun ce ba za su amince da wani rabon muƙamai da babu adalci da gaskiya a ciki ba.
Waɗanda su ka sa hannu a sanarwar sun haɗa da Sanata Ibrahim Shekarau (APC-Kano Central), Sanata Barau Jibrin (APC-Kano North), Tijjani Jobe (APC- mazaɓar D/Tofa/Rimingado ), Nasiru Gabasawa (APC- mazaɓar Gezawa/Gabasawa ), Haruna Dederi (APC- mazaɓar Karaye/Rogo ), Sha’aban Sharada (APC- mazaɓar Kano Municipal ) da kuma Shehu Dalhatu (Shugaban Buhari Support Group).
A sanarwar, ƴan tsagin Shekarau ɗin, wanda a ka laƙanawa sunan G-7, sun ce, “Mu waɗanda mu ka rattaba hannu a kan wannan sanarwa, mu na kara jaddada goyon bayanmu da sadaukarwarmu ga ci gaban manufofin jam’iyyarmu ta APC mai albarka a Jihar Kano da ma Nijeriya baki ɗaya.
“Kowa ya san irin kokarin da Shugabancin jam’iyyarmu ta ƙasa ya samar da nufin lalubo hanyoyin da za a bi wajen magance rikice-rikicen da suka dabaibaye jam’iyyarmu mai albarka a Jihar Kano. Muna yaba wa wannan gagarumin ƙoƙari da Shugabancin jam’iyyar na ƙasa ke yi.
“Mu na so mu baiyana, ba tare da shakka ba, cewa, har zuwa wannan lokacin da aka fitar da wannan sanarwa, babu wani mataki na karshe da aka ɗauka ko a ka cimma a ƙoƙarin sulhun da ya ke gudana.
“Yayin da muke jiran mu ga ƙudurin rabon muƙaman da shugabancin jam’iya na ƙasa zai gabatar, muna tabbatar wa ɗumbin magoya bayanmu cewa za mu yi nazari sosai a kan wadannan ƙudirin, kuma za mu amince da abin da ya dace kawai, na gaskiya da adalci ne kawai domin tabbatar da an baiwa kowa hakkin sa a jam’iyyarmu da kuma karfafa hadin kan ta.
“Duk da cewa mun samu nasara a hukunce-hukunce guda biyu a cikin Shari’a mai lamba FCT/HC/CV/2030/2021 na 30/11/2021, da ta FCT/HC/CV/2532/2021 na 17/12 /2021 dangane da shugabancin jam’iyyar a jihar mu.
“Muna kira ga dukkan ƴan jam’iyya a jihar Kano da su kwantar da hankula da kuma yin biyayya ga jam’iyyar har sai an kawo ƙarshen yunkurin da a ke na sulhu.
“Mu na gode muku bisa goyon baya da addu’o’in ku yayin da mu ke ci gaba da tsayawa kan gaskiya da adalci a cikin jam’iyyar,” in ji sanarwar.