News
Tun 2011 a ke bincike na a kan Boko Haram — Madu Sheriff
Daga kabiru basiru fulatan
Tsohon Gwamnan Jihar Borno, Ali Modu Sheriff ya ƙaryata rahotannin da a ke yaɗawa cewa ya na da hannu a Boko Haram, in da ya ce tun 2011 da ya bar mulki jami’an tsaro ke bincikar sa.
Daraktan neman zaɓen shugaban jam’iyar APC na Sheriff, Victor Lar ne ya ƙaryata zargin a wata ganawa ta musamman da Kamfanin Daillancin Labarai na ƙasa, NANa Abuja a jiya Lahadi.
Ya ce Sheriff, na gaba-gaba wajen neman kujerar shugaban jam’iyar APC na ƙasa kuma ya yi mulkin jihar Borno sau biyu, bashi da wata alaƙa da Boko Haram.
Ya ce babu sunan Sheriff a jerin sunayen masu ɗaukar nauyin Boko Haram da Dubai ta saki, inda ya nanata cewa tun 2011 bayan ya bar mulki jami’an tsaro ke tuhumar sa kuma ba a sake shi da wani laifi ba.
“Da ya na cikin masu ɗaukar nauyin Boko Haram a da tuni an yi masa hukunci ko kuma da tuni an fallasa shi.
“Sabo da haka ina ƙalubalantar duk wani mai zargin sa da ya zo da wata shaida gamsashshiya a kan hakan,” in ji Lar.