Connect with us

News

Jami’an NDLEA Sun Cafke Wani Matashi Bisa Zargin Boye Miyagun Ƙwayoyi A Al’aurarsa A Kano

Published

on

1781595463294

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen Jihar Kano ta cafke wani matashi da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi bayan an same shi da wasu ƙwayoyi da ya ɓoye a cikin wandon sa domin kauce wa ganowa.

Jami’in Hulɗa da Jama’a na hukumar a Kano, Sadiq Muhammad Maigatari, ne ya bayyana hakan ta wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook .

Advertisement

Gwamnoni Da Ministoci Za A Koma Kai Wa Hari Nan Gaba —Tsohon Hafsan Sojin Nijeriya

A cewar Maigatari, jami’an hukumar sun yi nasarar kama matashin ne yayin wani samame da suka gudanar, inda suka gano miyagun ƙwayoyin da ya ɓoye a wani sashe na jikinsa domin yaudarar jami’an tsaro.

Advertisement

“Wannan shi ne abin da ake kira dabara ta masu safarar miyagun ƙwayoyi a wannan zamani. Mun cafke wanda ya ɓoye miyagun ƙwayoyi a cikin al’aurarsa da nufin kauce wa binciken jami’anmu,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa hukumar za ta ci gaba da ƙarfafa yaƙi da safarar miyagun ƙwayoyi a faɗin jihar tare da tabbatar da cewa masu hannu a wannan haramtacciyar sana’a sun fuskanci hukunci bisa tanadin doka.

Advertisement

Maigatari ya kuma buƙaci jama’a su ci gaba da bai wa NDLEA haɗin kai ta hanyar kai rahoton duk wani motsi da ake zargi yana da alaƙa da safara ko fataucin miyagun ƙwayoyi.

 

Advertisement

 

AMINIYA

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending