Connect with us

News

Sabuwar Shekarar Musulunci: Falgore Ya Taya Al’ummar Musulmi Murna, Ya Sake Jaddada Kudirin Majalisar Kano Na Yi Wa Jama’a Aiki

Published

on

1749221874472 (1)

Shugaban Majalisar Dokokin Jihar Kano, Rt. Hon. Jibril Isma’il Falgore, ya taya al’ummar Musulmi murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1448 Hijiriyya, inda ya bukace su da su yi amfani da wannan lokaci wajen ƙarfafa imani, neman gafarar Allah da kuma kyautata hulɗa da juna.

A wata sanarwa da sakataren yaɗa labaransa, Kamaluddeen Sani Shawai, ya fitar ranar Talata, Falgore ya bayyana sabuwar shekarar Musulunci a matsayin wata dama ta yin nazari kan rayuwa, godiya ga Allah da kuma sake ɗaura damara wajen aikata alheri.

Advertisement

Jami’an NDLEA Sun Cafke Wani Matashi Bisa Zargin Boye Miyagun Ƙwayoyi A Al’aurarsa A Kano

Ya ce fara watan Muharram, wanda shi ne farkon watan kalandar Musulunci, na tunatar da muminai muhimmancin tsayawa kan tafarkin Allah tare da nisantar duk wani abin da zai jefa su cikin saɓo.

Advertisement

Falgore ya yi addu’ar Allah Ya sanya shekarar 1448AH ta kasance mai cike da albarka, zaman lafiya da ci gaba ga al’ummar Kano da Najeriya baki ɗaya.

“A madadin Majalisar Dokokin Jihar Kano, ina taya al’ummar Musulmi murnar sabuwar shekara. Muna roƙon Allah Ya sanya ta zama shekarar albarka, ƙarfafa imani, ƙaunar juna da kwanciyar hankali a tsakanin al’umma,” in ji shi.

Advertisement

Ya kuma yi kira ga jama’a da su dage wajen aikata ayyukan alheri, tare da neman kariyar Allah daga dukkan nau’o’in fitintinu da miyagun ayyuka.

Shugaban Majalisar ya kuma sake jaddada kudirin Majalisar Dokokin Jihar Kano na ci gaba da sauke nauyin da kundin tsarin mulki ya ɗora mata, yana mai tabbatar da cewa ‘yan majalisar za su ci gaba da samar da dokoki da tsare-tsaren da za su inganta rayuwar al’umma tare da haɓaka ci gaban jihar.

Advertisement

Har ila yau, ya yabawa Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa ƙoƙarinsa wajen aiwatar da ayyukan raya jihar, tare da taya shi da daukacin al’ummar Kano murnar sabuwar shekarar Musulunci.

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending