Connect with us

News

Gwamnatin Katsina Ta Haramta Sana’ar POS, Bunburutu Da Cajin Waya ‎

Published

on

images (2)

‎Gwamnatin Jihar Katsina ta sanar da wasu sabbin matakan tsaro da suka haɗa da haramta sana’ar POS, wuraren cajin waya na kasuwanci da kuma safarar man fetur a cikin jarkoki, a ƙoƙarinta na daƙile ayyukan ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane a jihar.

‎Matakan na ƙunshe ne a cikin wata Dokar Zartarwa da Gwamna Dikko Umaru Raɗɗa ya sanya wa hannu, bayan wani zama na gaggawa da ya gudanar tare da shugabannin hukumomin tsaro, sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki kan matsalar tsaro.

Advertisement

Sabuwar Shekarar Musulunci: Falgore Ya Taya Al’ummar Musulmi Murna, Ya Sake Jaddada Kudirin Majalisar Kano Na Yi Wa Jama’a Aiki

‎Babban Sakataren Yaɗa Labaran Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Kaula Mohammed, ya bayyana a wata sanarwa cewa dokar ta haramta gudanar da harkokin POS, wuraren cajin waya da kuma haya da babura a ƙananan hukumomin Matazu da Musawa nan take.

Advertisement

‎Sanarwar ta ce bayanan sirri da rahotannin jami’an tsaro sun nuna cewa wasu daga cikin cibiyoyin POS da wuraren cajin waya ana amfani da su wajen sauƙaƙa harkokin kuɗi da sadarwa ga masu aikata laifuka.

‎Haka kuma, gwamnatin ta haramta sayarwa da jigilar man fetur a cikin jarkoki a faɗin jihar, bayan rahotannin da suka nuna cewa ana amfani da irin wannan hanya wajen kai wa ’yan bindiga man fetur da sauran kayan tallafi a maboyarsu da ke cikin dazuka.

Advertisement

‎“Bayanan tsaro sun nuna cewa safarar man fetur a cikin mazubai na taka muhimmiyar rawa wajen ci gaba da ayyukan ta’addanci, lamarin da ya sa gwamnati ta ɗauki matakin katse hanyoyin samun kayayyakin da masu laifin ke amfani da su,” in ji sanarwar.

‎Gwamnatin ta kuma bayyana cewa hana haya da babura a Matazu da Musawa zai taimaka wajen rage zirga-zirgar ’yan bindiga da masu garkuwa da mutane, waɗanda galibi ke amfani da babura wajen gudanar da ayyukansu.

Advertisement

‎Gwamna Raɗɗa ya ce gwamnatinsa ba za ta yi ƙasa a gwiwa ba wajen ɗaukar duk matakan da suka dace domin kare rayuka da dukiyoyin al’umma, yana mai jaddada cewa yaƙi da rashin tsaro na ci gaba da kasancewa a sahun gaba na manufofin gwamnatinsa.

‎Ya kuma yi kira ga al’ummar jihar da su ci gaba da ba jami’an tsaro cikakken haɗin kai ta hanyar bin sabbin umarnin da kuma bayar da sahihan bayanai da za su taimaka wajen gano masu aikata laifuka.

Advertisement

‎Gwamnan ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu da karya dokar zartarwar zai fuskanci hukuncin da doka ta tanada, yana mai tabbatar da cewa gwamnati ba za ta yi sassauci ga masu karya doka ba.

 

Advertisement

 

 

Advertisement

Aminiya

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending