Hukumomi a jihar Karnataka da ke kudancin kasar India sun rufe dukkanin manyan makarantu da kwaleji-kwaleji na tsawon kwana uku, sakamakon karuwar zanga-zanga da ake yi kan mata ɗalibai Musulmai da ke sa hijabi.
Babban ministan ilmi na jihar, Basavaraj Bommai ya buƙaci jama’a da su kwantar da hankalinsu.
‘Yan sanda sun yi amfani da kulake domin tarwatsa daliban masu zanga-zanga da ke jifa da duwatsu a wasu sassan jihar.
A ‘yan makonnin da suka gabata ne dai al’amarin ya fara, bayan da wasu kwaleji-kwaleji suka hana mata ɗalibai Musulmai sanya hijabi su shiga azuzuwa domin ɗaukar darasi.
Hukumomin makarantun dai sun bayar da dalilinsu na hana sanya hijabin da ya yi karo da tsarin kayan bai ɗaya na ‘yan makaranta.