Yan wasan Chelsea da ba a yi wa allurar rigakafin korona za su rasa damar buga wasan zakarun Turai da kungiyar za ta buga da Lille ta Faransa a wata mai zuwa.
Hakan ya biyo bayan matakin hukumar kwallon kafa ta Turai na yin garambawul kan dokokinta na yaki da korona.
Dama hukumomin Faransa sun hana duk wanda ba a yi wa rigakafin ba shiga kasar.
Chelsea ta so mika bukatar mayar da wasan zuwa wata kasa don samun damar amfani da dukkanin ‘yan wasanta, to amma matakin na UEFA na nufin hakan ba zai yiwuwa ba.
Kungiyar ta Stamford Bridge za ta buga wasan farko da Lille a London ranar 22 ga watan Fabrairu, sai kuma ta je wasan ramako Faransa ranar 16 ga watan Maris.
To amma kawo yanzu Chelsea wadda yanzu haka ke Abu Dhabi don buga gasar zakarun kungiyoyin duniya ba ta bayyana ‘yan wasan da ba a yi wa rigakafin ba.
Mai horar da kungiyar Thomas Tuchel ya ce wannan matsala ce da za ta iya shafar makomar wasansu a wannan mataki, ganin cewa za su tafi buga gasar zakarun Turan ba tare da wasu manyan ‘yan wasa ba.