Yarima Charles mai jiran gadon Masarautar Birtaniya ya kamu da cutar korona har ma ya killace kan sa, a cewar fadarsa ta Clearance House cikin wata sanarwa a Twitter.
An sanar da labarin kamuwar tasa ne jim kaɗan kafin ya fita zuwa Winchester don halartar wani biki.
A ranar Laraba yariman da matarsa Camilla sun gaisa da mutane a wurin wata liyafa a gidan ajiye kayan tarihi na British Museum.
A ranar Alhamis gwaji ya nuna Camilla ba ta ɗauke da cutar. Wannan ne karo na biyu da Yarima Charles ya kamu da cutar.
A watan Maris na 2020 ne yariman mai shekara 73 ya fara harbuwa da cutar.