Babban Bankin Najeriya CBN ya ce zai daina sayar wa bankunan kasuwanci na ƙasar kuɗaɗen ƙasar waje nan da ƙarshen shekarar 2022.
Gwamnan CBN Godwin Emefiele ne ya bayyana hakan a taron manema labarai da ya yi jiya Alhamis, yana mai cewa wajibi ne bankunan su fara nemo kuɗaɗen ƙasar wajen da kansu ta hanyar kasuwancin abin da suka fitar zuwa ƙasashen wajen.
“Lokacin yana zuwa ƙarshe, idan kwastomominka na buƙatar dala miliyan 100 ko miliyan 200, sai ka zo CBN ya ɗebi duk dalolin ya ba ka. (Wannan) na zuwa ƙarshe kafin ko kuma zuwa ƙarshen shekarar nan.,” in ji shi.
“Za mu faɗa musu cewa kar ku sake zuwa wajen CBN (neman dala), ku je ku nemo kuɗaɗenku. Idan kuɗin suka zo mu kuma sai mu sayar muku su a kan ribar kashi 5 cikin 100, ku kuma sai ku sayar wa kwastomomin da ke son dala miliyan 100.
“Amma dai ku ce za ku ci gaba da zuwa CBN don ya ba ku dala, za mu dakatar da wannan.”
A shekarar 2021 ne babban bankin ya dakatar da sayar wa kamfanonin ‘yan kasuwa masu harkar canji kuɗaɗen ƙasar waje, inda ya koma sayar wa bankuna kaɗai.