Sports
Najeriya ta zama kasa ta 3 a Afirka wajen kwarewa a kwallon kafa. FIFA

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Sabon jadawalin da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar ya nuna cewar, Najeriya ta haura matakai hudu, inda a yanzu ta koma kan matsayin kasa ta 32 a duniya da ta fi kwarewa a kwallon kafa, duk da cewa ta fice daga gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Kamaru tun a zagaye na 2.
Hukumar ta FIFA ta kara da cewar, a Nahiyar Afrika, Najeriya ce ta uku a bayan Morocco ta biyu, sai kuma Senegal ta farko wadda ta lashe gasar cin kofin kasashen na Afirka.
Sauran kasashen da ke bayan Najeriya sun hada da Masar da Tunisi, sai Kamaru da Aljeriya da Mali da kuma Ivory Coast.
A halin yanzu Senegal tana matsayi na 18 a duniya bayan ta zama zakara a gasar AFCON da Kamaru ta karbi bakunci.