Sports
Wasanni: Yan sanda a Brazil Sun kama matashin dake kutse a asusun ajiyar bankin Dan wasa Neymar.
Daga Muhammad Muhammad zahraddini
‘Yan sandan Brazil sun sanar da kama wani matashi mai kimanin shekaru 20 da suka yi imanin cewa yana kutsawa asusun bankin dan wasan kwallon kafar kasar Neymar Junior yana wawure kudade sannu a hankali, inda ya sace jummular sama da dala dubu 40.
‘Yan sanda a Sao Paulo sun ce wanda ake zargin ya yi kutse ne a wani banki da ba a bayyana sunansa ba inda dan wasan Paris St-Germain (PSG) da Brazil da mahaifinsa da kuma manajan sa ke da asusu.
Ko da yake rundunar ‘yan sandan ba ta bayyana sunan dan wasan ba a cikin sanarwar, amma wani jami’in da ke kula da lamarin ya ce Neymar ne.
Shidai wannan matashi ya kware a harkar kutsen tare da shiga asusun ajiyar fitattun mutane, inda yakan zare Kannan kudi ta yadda baza ayi saurin ganewa ba.