News
An yi gobara a gidan Sheikh Ahmad Gumi da ke Kaduna
Daga kabiru basiru fulatan
An yi gobara a gidan Sheikh Ahmad Gumi da ke Kaduna
..An yi gobara a gidan Sheikh Dakta Ahmed Gumi da ke garin Kaduna.
Jaridar Daily Trust a Najeriya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Asabar.
Babu tabbaci kan abin da ya jawo gobarar hakazalika babu ƙarin bayani kan ko akwai wanda ya samu rauni ko kuma ya rasa ransa.
Wani bidiyo da malamin ya wallafa a shafinsa na Facebook ya nuna yadda ake ƙoƙarin kashe gobarar.
Haka kuma a cikin bidiyon an ga malamin na duba sassan gidan da gobarar ta shafa