News
Gwamnatin Jigawa zata fara bawa masu juna biyu N5,000 a wata.
Daga Muhammad Muhammad zahraddini
Dutse – Gwamnatin Jihar Jigawa ta bayyana cewa komai ya kankama don fara biyan mata masu juna biyu sama da mutum 5000 kudi dubu biyar-biyar a wata, Mataimakain Gwamanan Jihar, Mallam Umar Namadi, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar, rahoton Aminiya.
Namadi yace jihar ta bullo da shirin ne domin ya taimaka wa mazauna karkara don su rika zuwa awon ciki a asibiti kafin haihuwa.
Ya ce gwamnatin Muhammad Badaru ta sanya wannan kudi cikin kasafin kudin 2022 da Gwamnan ya rattafa hannu.
Ya kara da cewa an bude wa kimanin mata 3,800 asusun ajiya na banki kuma za a fara biyansu a watan Fabrairun 2022, Hakazalika suna kokarin yiwa sauran matan 1200.