News
Jiragen sojin Nijeriya sun hallaka ƴan ta’adda 20

Daga yasir sani abdullahi
Dakarun sojin sama na Nijeriya, ƙarƙashin’Operation Thunder Strike’, sun hallaka ƴan ta’adda 20 a yankin Makarantar Koyon aikin Soja.
Wasu sahihan majiyoyi na sirri sun shaidawa jaridar PRNigeria cewa an ga ƴan fashin daji a babura sama da 50 sun nufi Makarantar Koyon aikin Soja ɗin da ke Jihar Kaduna a ranar Alhamis da yamma.
A tuna cewa a watan Yunin 2021 ne dai ƴan bindiga su ka kutsa kai cikin makarantar, su ka kashe sojoji 2 sannan su ka yi garkuwa da Kaftin ɗin Sojan Ƙasa a yayin harin.
PRNigeria ta jiyo cewa bayan wasu bayanan sirri na yunƙurin kai harin kan makaranta, sai a ka tashi jiragen yaƙi 2 na Rundunar Sojin Sama, NAF su ka dirar wa ƴan ta’addan da a ke tsammanin sun taso ne daga ƙauyen Damari a Ƙaramar Hukumar Birnin Gwari.
An hango ƴan fashin dajin su da yawa a wasu tantuna na wucin-gadi da kuma baburan wajen 50.
Ganin jiragen ne ya sanya ƴan ta’addan su ka tarwatse suna neman mafaka a kuryar jeji, inda a riƙa yi musu ruwan wuta, inda a ka hango wadanda ba su mutu ba su na neman tsira.
A ranar Juma’a ne a ka samu bayanai da ga sojojin ƙasa da mazauna ƙauyuka cewa ƴan ta’addan 20 ne su ka mutu.