Ministan yada labarai na Najeriya Alhaji Lai Muhammad ya caccaki Twitter tare da zargin kamfanin da zama mai fuska biyu.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, Alhaji Lai ya ce, ya yi wannan zargin ne biyo bayan zanga-zangar masu manyan motoci da ke faruwa a Canada saboda dokar hana zirga-zirga da aka sanya dalilin annobar korona, wanda hakan ya kawo tsaikon kasuwanci da Amurka.

Masu zanga-zangar sun toshe manyan titunan birnin Ontario, wanda yakan ya janyo bacin rai ga kamfanoni da kuma daidaikun mutane har ma da gwamnati.
Gwamnatin kasar ta bayyanasu a matsayin ” ‘yan ta’adda ko kuma wadanda suke rikici da gwamnati”.
Kamfanin asusun da ke tara kudi ya rufe asusun masu zanga-zangar bayan sun tara dala miliyan 10, haka shi ma Twitter ya dakatar da shafinsu yayin da gwamnatin Ontario ta kulle asusunsu mai dauke da miliyoyin kudi da suka tara a intanet.
Kazalika Jim Waston wanda shi ne mai garin Ottawa, ya ayyana dokar tabaci a birnin a wani mataki na dakile barazanar masu zanga-zangar.

Sai dai duk ya faka wadannan hujjoji ne domin tuna baya lokacin zanga-zangar EndSars, da kasancewar Canada a matsayin daya daga cikin kasashen da suka nuna goyon bayansu ga masu zanga-zangar.#
Da kuma matakin da Twitter ya dauka ya dauka na goge sakon shugaba Buhari da taimaka musu wajen tattara kudade da za a yi amfani da.
“Sune dai mutanen da suke kuma nisanta kansu daga samu zanga-zanga a Canada kuma suka hana masu zanga-zangar damar amfani da kudadensu.”Ba wai muna farinciki da abin da ke faruwa ba ne a Canada, a’a muna so muja hankali ne kan yadda suke samun fuska biyu kan lamari daya, yadda suke kallon zanga-zanga a Najeriya da kuma a kasashen yamma” in ji Alhaji Lai.
Ba za mu bar wani ya lalata kasarmu ba, karkashin inuwar zanga-zanga ko kuma a yi da sunan karyar ‘yanci. Mu Najeriya muka sa a gaba farko.