News
Shugaban Amurka, Joe Biden, ya tabbatar da samar da motoci masu lantarki ga Amurkawa

Daga Muhammad Muhammad zahraddini
Shugaban Amurka, Mista Joe Biden, yana ta yunƙurin samawa Amurkawa hanyoyin da za su wataya, musamman a wannan lokaci da fasahar ƙere-ƙere ta duniya ta mayar da hankali a kan motoci masu amfani da lantarki.
A ƙoƙarin shugaban na ganin ba a bar Amurkan a baya ba, ya yi wa ‘yan ƙasar alƙawarin samar da wuraren yin cajin motocin a cikin sauƙi domin sauƙaƙawa Amurkawa.
Ko me ‘yan Najeriya za su ce game da wannan tagomashi na shugaban Amurka ga Amurkawa? ‘Yan Najeriya kuma ga shi ana ta fama da haƙilon gurɓataccen man fetur.