News
Shekaru 46 da kashe Shugaban Kasa Janar Murtala Ramat Muhammad.
Shekaru 46 da kashe Shugaban Kasa Janar Murtala Ramat Muhammad.
Mai girma Walin Kano Alh. Mahe Bashir Wali wanda ya kasance makusanci ga tsohon shugaban mulkin soja wato Marigayi Gen. Murtala Ramat Muhammad, ya bada labarin cewa Gen. Murtala Ramat Muhammad mutum ne mai kwarjini wanda ko kaɗan babu alamar wasa a tattare da shi, yace da zarar mutum ya haɗa ido dashi idan har bashi da gaskiya, to sai dai a ga mutum ya hau tsuma yana kyarma.
Sannan kuma ance General Murtala Ramat Muhamad mutum ne da yake son yin abu da gaggawa ba tare da ɓata lokaci ko jinkiri ba, don haka ne ma akoda yaushe yake yawan maimaita kalmar “DA GAGGAWA”, kamar yanda marigayi Yusuf Maitama Sule (Ɗan Masanin Kano) ya faɗa.
Marigayi Sunday Awoniyi yace “Gen. Murtala Ramat Muhammad shi mutum ne wanda ko kaɗan bai cika son wasa ba, don haka ko tafiya da zugar motoci baya yi, haka kuma baya kunna jiniya a lokacin da yake fita ko dawowa, sannan kuma daga shi sai direbansa suke zuwa Kano tun daga Lagos a motarsa ba ta gwamnati ba, wato tafiyar sama da kilomita dubu 1000”.
General Murtala Ramat Muhammad mutum ne wanda yake da ƙarfin hali da rashin nuna tsoro ga kuma kwarjini, kamar yadda Marigayi Sunday Awoniyi yace; “shi mutum ne wanda tun lokacin da yana makaranta a Barewa College Zaria baya faɗa da sa’anninsa, sau da dama za’a samu yana faɗa da na gaba dashi musamman akan zalunci.
General Murtala Ramat Muhammad shine shugaba ɗaya tilo wanda dukkanin ƙabilu da yarukan Najeriya suke matuƙar girmamawa, saboda a ɗan lokacin da ya mulki Najeriya yayi ƙoƙari wajen tafiyar da mulkinsa bisa adalci, ba tare da nuna wani bambanci ƙabila ko yare ba, wanda hakan yasa ya zama shugaba ɗaya tilo da kowace ƙabila da yare suke ƙaunar sa. Kuma shine shugaban mulkin soja da aka taɓa sanya shi ajikin kuɗi tare da kakinsa na soja, saboda martabawa da kuma girmamashi da ake yi.
Kamar yanda cikakkun masana suka yi bayanin cewa ana son shugaba ya kasance jarumi mai kwarjini, maras tsoro da kuma ƙarfin hali da ƙarfin zuciya, to haƙiƙa General Murtala Ramat Muhammad ya cika dukkan waɗannan abubuwa da suka sanya zai iya zama kowane irin shugaba.
An kashe General Murtala Ramat Muhammad a ranar juma’a 13-02-1976 a birnin Lagos.
Muna addu’ar Allah (S.W.T) ya jikan General Murtala Ramat Muhammad, Ya kai rahama da haske cikin kabarinsa, Ya sanya mutuwa ta zamo hutu a gareshi. Muna roƙon Allah (S.W.T) Ya arzurta mu da mutane masu ƙarfin hali da ƙwazo irin nasa ko kuma waɗanda ma suka fi shi.
Allah (S.W.T) Ya bamu zaman lafiya da kwanciyar hankali mai ɗorewa a wannan ƙasa ta mu Nigeria.
