News
Rikicin APC a Kano: Uwar jam’iyya ta maida mu ƴaƴan bora — Shekarau

Daga yasir sani abdullahi
Bayan awanni da Kotun Ɗaukaka Ƙara ta shure nasarar da ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau ta yi a Babbar Kotu a Abuja, ta kuma tabbatar da shugabancin ga tsagin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje a jiya Alhamis, Sanatan ya ce Uwar Jam’iyya ba ta yi musu adalci ba.
A wani saƙon murya da ya fitar ta kafar Whatsapp a jiya Alhamis, Shekarau ya ce shelkwatar APC ta maida wasu ƴan jam’iyar APC ƴaƴan mowa, wasu kuma ƴaƴan bora a Jihar Kano.
A cewar sa, ɓangaren da ya ke jagoranta ya yi watanni biyu da nasarar samun shugabanci a kotu, amma uwar jami’ya ba ta ba su takardar shaidar zama shugaban jam’iyya ba.
Amma, in ji Shekarau, ƙasa da awanni biyu da Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta yanke hukunci a jiya Alhamis, har Shelkwatar APC ɗin ta miƙa wa Abdullahi Abbas takardar shaidar zama shugaban jam’iyya na jiha.
“Mu da mu ke da hukuncin kotu kusan wata biyu, jam’iyya ba ta yarda ta karbi wannan hukunci ba ta bamu shaidar takardar cewa mu ke da shugabancin jam’iyya. Mu ka nuna girmamawa. Mu ka saurari kiran jam’iyya mu ke zama a teburin sulhu.
“Amma sai ga shi, a yau, cikin ƙasa da awa biyu da yin hukunci, shugabancin jam’iyya ya kira ɓangaren mai girma Gwamna an basu takarda cewa su ke da shugabancin jam’iyya a Jihar Kano.
“Wannan ya nuna kamar a kwai ƴan bora da ƴan mowa a cikin jam’iyya.
“Mun ɗauka, sanda mu ke da hukunci a hannun mu, za a saurare mu, alabashshi, idan kotu ta gaba da wacce ta bamu ta ce ba haka ba, sai a karɓe a baiwa waɗanda ta ce a baiwa. In mun ga dama mu kai gaba ko mu ce mun karɓa. To amma sai a ka yi abinda ya nuna cewa a kwai rashin adalci a ciki,” in ji Shekarau.
Ya kuma ƙara da cewa sun baiwa lauyoyin su umarnin yin nazari a kan hukuncin na Kotun Ɗaukaka Ƙara, inda ya ce da zarar sun kammala nazarin, za su shigar da ƙara a Kotun Ƙoli.
Tsohon Gwamnan kuma ya nuna rashin jin daɗin sa a bisa furuce-furuce na ɓatanci da ya ce Ganduje ya yi bayan hukuncin Kotun Ɗaukaka Ƙarar, inda ya ce ” Wannan bai nuna girma na shugabanci ba, kuma bai nuna buƙatar haɗin kai da samar da sulhu a tsakankanin ƴan jami’ya ba da kuma al’ummar Jihar Kano baki ɗaya.”
“Don haka mu na kira ga jam’iyya da su sake duba wannan al’amari da kuma tabbatar da cewa an yi wa kowa adalci a cikin tsari na shugabancin jam’iyya,” in ji shi.