News
Buhari ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren da ake kaiwa ‘yan Sanda da Kabilu a fadin Najeriya.

Daga Muhammad Muhammad zahraddin
Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi Allah-wadai da yawaitar kashe-kashe da munanan hare-haren da ake kaiwa ‘yan sanda da tsirarun kabilu kan rahotannin baya-bayan nan a jihohin Enugu, Imo, Abia, Zamfara da Ogun, kamar yadda babban mai taimaka wa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai Garba Shehu ya fitar.
Sanarwar ta ce, “Ina Allah wadai da wadannan munanan ayyukan ta’addanci tare da yin addu’a ga rayukan wadanda suka rasu.
“Dole ne kotunan kasar su yi amfani da hukunci mai tsauri a karkashin dokokinmu ga wadanda suka aikata wadannan munanan laifuka.
“Kashe-kashen da ake yi da sunan al’ada, tada zaune tsaye a siyasance da kiyayyar kabilanci ba su dace da tsarin addininmu da al’adu ba. Babu wani mutum da yake da hakkin daukar doka a hannunsa.
Jaridar indaranka ta rawaiti A halin da ake ciki, shugaba Buhari ya yabawa gwamnatin jihar Abia bisa matakin da ta dauka na mayar da martani kan harin da aka kaiwa ‘yan kasuwa a sabuwar kasuwar shanu dake karamar hukumar Ukwa a kwanakin baya.
Ya jajanta wa iyalan mutanen da aka kashe da kuma wasu da suka yi asarar dukiyoyi yayin harin.