News
YANZU-YANZU: Mai shekaru 102 ta bayyana aniyar tsayawa takarar shugaban kasa a Nijeriya
Daga kabiru basiru fulatan
Wata tsohuwa ‘yar Najeriya mai shekaru 102, Nonye Josephine Ezeanyaeche, ta bayyana aniyarta ta tsayawa takarar shugaban kasa a shekarar 2023.
Ezeanyaeche ta bayyana aniyar ta ne a wata ziyarar ban girma da ta kai wa tawagar gudanarwar gidan talabijin na Najeriya, NTA.
A yayin ziyarar ta bayyana shirin tsayawa takara a zaben shugaban kasa a 2023.
Jaridar indaranka ta rawaito cewa Dattijuwar mai shekara ɗari da ake kira da “Mama Africa”, ta fito ne daga Aguata, jihar Anambra kuma ita ce ta kafa ƙungiyar ‘Voice for Senior Citizens of Nigeria’.
“Idan ‘yan Najeriya suna jin kunyar kauracewa shiga siyasa, ta ce a shirye take ta tsaya takara. Tuni ta shirya wa kanta tsare-tsare. Tana da hangen nesa. Idan nagari ba su fito takara ba…”
Ezeanyaeche kamar yadda ta fada a cikin harshen Igbo, “Idan kana da yaro namiji ko mace, yi kokarin horar da su su wuce nasarorin da ka samu.”