Connect with us

News

Jihohi 33 Da Al’ummomi Sama Da 14,000 Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A 2026 — Gwamnatin Tarayya 

Published

on

Ambaliya a Neja Mutum 110 sun mutu, ruwa ya rushe gidaje fiye da 50 a Mokwa

Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta yi gargaɗin cewa jihohi 33 da kuma al’ummomi sama da 14,000 na cikin haɗarin fuskantar ambaliyar ruwa a shekarar 2026, yayin da ake shirin shiga lokacin damina a sassan ƙasar.

Ministan Albarkatun Ruwa da Tsabtar Muhalli, Joseph Utsev, ne ya bayyana hakan a Abuja ranar Laraba, lokacin gabatar da hasashen ambaliya na shekara-shekara da hukumomin ruwa suka shirya.

Advertisement

Jihohi 33 Da Al’ummomi Sama Da 14,000 Na Fuskantar Barazanar Ambaliya A 2026 — Gwamnatin Tarayya 

A cewarsa, kimanin al’ummomi 14,118 da ke cikin ƙananan hukumomi 266 a jihohi 33, har da Babban Birnin Tarayya (FCT), na cikin babbar barazanar ambaliya a bana.

Advertisement

Jihohin da abin ya shafa sun haɗa da Abia, Adamawa, Anambra, Bauchi, Bayelsa, Benue, Borno, Cross River, Delta, Ebonyi, Edo, Enugu, Gombe, Imo, Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Kogi, Kwara, Lagos, Nasarawa, Niger, Ogun, Ondo, Osun, Oyo, Plateau, Rivers, Sokoto, Taraba, Yobe da Zamfara, tare da FCT.

Bugu da ƙari, rahoton ya nuna cewa akwai wasu ƙananan hukumomi 405 a jihohi 35 da ke cikin matsakaicin haɗarin ambaliya, sai kuma ƙananan hukumomi 77 a jihohi 24 da ake hasashen za su fuskanci ƙananan ambaliya a al’ummomi 923.

Advertisement

Sabon tsarin hasashen ambaliyar da aka gabatar a bana ya bambanta da na baya, inda aka fi mayar da hankali kan al’ummomi kai tsaye, maimakon jihohi da ƙananan hukumomi kawai, domin inganta shirin kariya da daukar matakan gaggawa.

A nasa jawabin, Ministan Muhalli, Balarabe Lawal, ya jaddada aniyar gwamnatin shugaba Bola Tinubu na ƙarfafa shirye-shiryen tunkarar bala’o’i, musamman ta fuskar daukar matakan kariya da kai dauki ga al’ummomin da ke cikin haɗari.

Advertisement

Rahoton ya zo ne a daidai lokacin da ake fara samun ruwan sama a sassa daban-daban na ƙasar, lamarin da ke ƙara tayar da hankalin jama’a kan yiwuwar aukuwar ambaliyar ruwa, wadda kan jawo asarar rayuka da dukiyoyi a duk shekara.

 

Advertisement

 

TRT AFRIKA 

Advertisement
Advertisements
Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Trending