Connect with us

News

Ga jerin abubuwan da za a tanada domin samun nasarar yin rijistar JAMB a 2022

Published

on

Official JAMB logo
Spread the love

Daga yasir sani abdullahi

 

 

Advertisement

ADIRESHIN E-MAIL: Dole ne mai yin rijista ya zama yana da adireshin email. Saboda haka yana da kyau a kirkiri adireshin email mai kyau kuma gajere idan zai yiwu, mai dauke da password mai karfi wadda ba za a manta ba.

LAMBAR WAYA: Dole ne mai shirin yin rijistar JAMB ko DE ya tanadi lambar waya tasa ta kansa, wadda yai rijista da sunansa, ma’ana mallakinsa ba ta aro ba.

MALLAKAR NIN NUMBER: Dole ne mai son yin rijistar JAMB ko DE ya mallaki lambar shaidar zama dan kasa, NIN. Kuma ya zama a lokacin NIN din ya yi rijista da sunansa da shekarunsa yanda suke, domin a bana, za a tura NIN ne wajen kirkirar PROFILE ba SUNA ba. Haka kuma lokacin rijista suna da shekara na kan NIN ne za su baiyana.

Advertisement

KIRKIRAR PROFILE: Dole ne mai yin rijistar ya kirkiri profile, kuma zai yi hakan ne ta hanyar tura wannan sako *55019*1*NIN# a kan layinsa na waya. Idan ya yi hakan zai samu sako mai dauke da sunansa da kuma profile code da zai amfani da shi wajen siyan JAMB ko DE da kuma cikewa.

NEMAN SHAWARA KAN ZABIN UNIVERSITY DA COURSE: Yana da matukar kyau, mai shirin yin rijistar JAMB ko DE ya nemi shawarar masana kan zabin da zai yi idan ya zo zaben jami’a da kuma course. Hakan yana kara tabbatar da nasarar da ake nema ta samun gurbin karatu da jami’ar da ta dace.

SIYAN ePINBayan an kammala wadancan na baya sai kuma siyan PIN wato lambar form din da za ta bayar da damar cike form din a yanar gizo idan an je CBT CENTRE.

Advertisement

JARABAWAR SIKANDIRE: Ga masu yin JAMB, Yana da matukar amfani a tanadi sakamakon jarabawar sikandire, idan kuma ba ta fito ba, to a tanadi lambobin jarabawar domin za a shigar da su domin yin rijistar.

KUDI: A bana ma kudin JAMB da DE bai canja ba, PIN = N3500, Littafi: N500, Kudin CBT = N700 jimilla N4,700.

Advertisement

Advertisement
Click to comment

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *